Rahama Sadau: ‘Na ji kamar zan mutu lokacin kullen korona’

Rahama Sadau

Hakkin mallakar hoto
@artssassin/Pixel Pitch

Image caption

Rahama ta ce mutane da dama suna son ta da aure

Fitacciyar tauraruwar Rahama Sadau ta ce ta ji kamar za ta mutu lokacin kullen korona saboda yadda take zaune wuri guda na tsawon watanni.

Ta bayyana hakan ne lokacin da muka yi wa hira ta musamman da ita a shafinmu na Instagram.

“Lokacin kullen sai dai mutum ya yi ta yin kame-make. Ka yi karatu ya ishe ka, ka yi kallo ya ishe ka, ka yi chatting ya ishe ka,” in ji ta.

Ta ce kullen ne ya sa ba a jin dukiyarta kwana biyu.

Har ila yau Rahama ta ce ta ji babu dadi a lokacin kuma ta ji “kamar za ta mutu.”

Ta ce sana’arsu tana bukatar tara jama’a kuma yanzu an hana yin hakan saboda wannan annoba saboda haka a cewarsa korana ta fi shafar su fiye da kowa.

Hakkin mallakar hoto
Pixel Pitch

Image caption

‘Ban daina yin fina-finan Nollywood ba’

Rahama ta ce ta kammala karatunta, inda ta karanta fannin Human Resource Management a kasar Syprus.

Ta ce karatun ne ya sa ba ta iya ci gaba da harkokin fina-finanta ba gadan-gadan.

Tauraruwar ta ce tana iya magana da harshe uku Hausa, Turancin Inglishi da kuma Indiyanci.

Rahama ta ce mutane da dama suna son ta da aure,”yawanci sai da ni dariya ko kuma na ce na gode,” in ji ta.

Sai dai ta ce ita ba ta da wani saurari a Kannywood a halin yanzu.

Ce-ce-ku-ce

Hakkin mallakar hoto
@artssassin/Pixel Pitch

Dangane da yadda take yawan jawo ce-ce-ku-ce Rahama ta ce hakan yana faruwa ne saboda yadda “duk abin da na yi duk kankantarsa mutane sai sun yi magana a kai,” in ji ta.

Rahama ta ce hakan ba ya sa ta damuwa “saboda mafiyawanci ban cika gani ba.”

“Idan na ga mutum daya ya fara magana mara dadi, fita nake yi gaba daya. Ba na ganin sauran, sai komai ya yi sauki. Wani lokacin kuma ina gani ban zan iya sa abu ya dame ni ba, abin da bai kai ya kawo ba,”a cewarta.

Fyade

Ta ce ba ta jin dadin yadda matsalar fyade take ci gaba tabarbarewa, ta ce abin yana daure maka kai.

“Nakan tambayi mutane wannan abin da ke faruwa da gaske ne… wasu za ka ga ‘ya’yansu suke wa. Wai duk na mene ne,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa “wannan abin bacin rai ne ba kadan ba.”

Ta bukaci hukumomi da su dauki manyan matakai don dakile matsalar kuma ta ce ya kamata kowa ya tashi tsaye kan batun.

Siyasa

Tauraruwar ta ce ita ba ta siyasa, ta ce ita ‘yar Najeriya ce kamar kowa duk abin da ta ya yi mata za ta iya magana a kai.

“Ni na san wanda na zaba ba sai zo na nuna haka ba, cewa ni na zabi wane ba. Ban sani ba ko a nan gaba zan fara siyasa, amma a yanzu a’a,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa “idan na jefa maka kuri’a, amma sai ka ki yin abin da ya kamata to zan fito na yi magana.”

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...