‘Pogba na son koma wa Barcelona, Madrid na son Alonso’

[ad_1]

Marcos Alonso

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Marcos Alonso

Real Madrid tana zawarcin dan wasan bayan Chelsea dan kasar Spain Marcos Alonso, mai shekara 27, bayan ta sha kaye a hannun abokiyar hamayyarta Atletico Madrid a wasan Super Cup, kamar yadda jaridar (Star)ta ruwaito.

Mataimakin shugaban Real Betis, Lorenzo Serra Ferrer, ya ce kungiyar ta Seville za ta so ta sayi dan wasan gaban Tottenham dan kasar Brazil, Lucas Moura, mai shekara 26, kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa, a cewar (El Desmarque – in Spanish).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Paul Pogba

Ita kuwa jaridar(Mail) cewa ta yi dan wasan tsakiyar Manchester United wanda ya lashe kofin duniya Paul Pogba yana son barin Old Trafford domin koma wa Barcelona.

Mourinho ya shaida wa Pogba cewa ya nemi tafiya idan yana son barin kulob din.

Dan wasan Faransan, mai shekara 25, ya mayar da martani cewa shi zai yi magana da kocin dan kasar Portugal ta bakin ejen dinsa, kamar yadda jaridar (Sun) ta ruwaito.

Har ila yau jaridar (Mirror) ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Manchester City din mai shekara 27 Kevin de Bruyne zai yi jinyar wata uku bayan ya ji rauni a gwiwarsa ta dama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kevin de Bruyne

Hakazalika jaridar (Mirror) ta ruwaito cewa Bayern Munich tana son sayen dan wasan Tottenham, mai shekara 29, Toby Alderweireld.

GolanArsenal,mai shekara 29, dan kasar Colombia David Ospina ya koma buga wasan aro a kungiyarNapoli, in ji (Guardian).

Mediasetta ruwato cewar Parma ta kusa sayen dan kasar Ivory Coast Gervinho, mai shekara 31, daga kungiyar kwallon kafa ta kasar China Hebei Fortune.

Liverpool ta ki tayin da Torino ta yi wa dan wasan tsakiyar Serbiya, mai shkeara 22, Marko Grujic.

Kulob din na Italiya ya so dan wasan ya buga masa wasan aro ne tsawon kaka daya da zabin sayensa kan kudi fan miliyan tara a kaka mai zuwa, in ji (Liverpool Echo).

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...