Peter Obi ya ziyarci Sheikh Gumi

Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyar Labour Party, Peter Obi da kuma mataimakinsa Datti Baba Ahmed sun kai ziyara ga Sheikh Ahmed Gumi a gidansa dake Kaduna.

Obi ya bayyana ziyarar ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter dauke da hotunan ziyarar.

Sai dai wallafa hotunan ke da wuya mutane suka fara ce-ce-kuce.

A baya dai da yawa daga cikin magoya bayan Obi sun kasance masu kausasa harshe akan shehin malamin. Kuma a yanzu suna ganin ba dai-dai bane Obi ya ziyarce shi.

More from this stream

Recomended