Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a wani Masallaci dake ƙauyen Larabar Abasawa a ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano
Obi wanda ya isa Kano ranar Lahadi ya zarce kai tsaye daga filin jirgin saman Mallam Aminu ya zuwa Asibitin Kwararru Na Murtala Muhammad inda wasu daga cikin mutanen suke samun kulawar likitoci.
Da yake duba marasa lafiyar Obi ya bayyana cewa lallai abun ya yi muni sosai kuma abun takai ci ne ace irin haka na faruwa a Najeriya a yanzu.
Ya ce dalilin ziyarar tasa shi ne nuna goyon baya ga kula da lafiyar mutanen da kuma duba yiyuwar hanyar da zai taimaka musu.
A karshe ya miƙa sakon taaziyarsa ga mutane da kuma gwamnatin Kano.