Peter Obi Ya Ziyarci Atiku Da Sule Lamido A Abuja

Peter Obi ɗantakarar shugaban ƙasa a jam’iyar LP a zaɓen shekarar 2023 ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a. Abuja ranar Litinin.

Atiku da ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyar PDP shi ne ya sanar da ziyarar cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ganawar da manyan ƴan siyasar biyu suka yi ita ce irinta ta farko da suka yi tun bayan kammala zaɓukan 2023.

Har ila yau Obi ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo a gidansa dake Abuja.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da aka fitar kan abun da ganawar ta mayar da hankali akai.

More from this stream

Recomended