
Tsohon gwamnan jihar Anambra, kuma mutumin da ya yiwa jam’iyyar Labour Party takarar kujerar shugaban kasa a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi ya sanar da shigarsa jam’iyar ADC.
Obi ya sanar da shigarsa jam’iyar ne a wurin wani taro da ya gudanar a jihar Enugu wanda ya samu halartar jiga-jigan yan siyasa da suka fito daga ciki da wajen yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Taron ya gudana ne a ranar Talata a otal din Nile Lake Resort dake Enugu.
“Muna kammala wannan shekarar dafatan cewa a shekarar 2026 zamu fara tafiyar ceto Najeriya,” a cewar Obi.
Shugaban jam’iyar ADC na kasa,Sanata David Mark na daga cikin waɗanda suka halarci wurin taron.
Sauran wadanda suka halarci wajen taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Emeka Ihedioha tsohon gwamnan jihar Imo wasu yan majalisar dattawa.

