Peter Obi ya gana da Bala Muhammad

Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyar Labour Party a zaben shekarar 2023 ya ziyarci gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin jam’iyar PDP, Bala Muhammad.

Ganawar ta su ta gudana ne a gidan gwamnatin jihar dake Bauchi a dai-dai lokacin da ake cigaba da raɗe-raɗin batun hadewar ƴan adawa ƙarkashin inuwar jam’iya guda gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Babu wani cikakken bayani kan abun da ganawar ta su ta mayar da hankali akai amma ana sa ran gwamna , Bala Muhammad zai yiwa yan jaridu bayani.

A ranar Laraba mai taimakawa shugaban ƙasa Bola kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala ya yi iƙirarin cewa nan gaba kaɗan fita Obi zai fice daga jam’iyarsa ta Labour ya koma jam’iyar APC mai mulki.

More from this stream

Recomended