PDP ta nisanta kanta da batun haɗakar jam’iyu

Gwamnonin da aka zaɓa ƙarkashin jam’iyar PDP sun ce jam’iyar baza ta hade da wasu jam’iyu ba domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Gwamnonin sun bayyana matsayar jam’iyar ta su ne a wani jawabin bayan taron da aka fitar ranar Litinin a ƙarshen taron da suka gudanar a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Amma gwamnonin sun ce jam’iyar PDP na maraba da duk wata jam’iya, kungiya ko kuma  wani mutum dake da niyar shiga jam’iyar domin kayar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

A ƴan kwanakin nan dai ana cigaba da tattaunawa da kuma samun karin kiraye-kiraye na jam’iyyun adawa su haɗe wuri guda domin ƙalubalantar jam’iyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Matsayar da gwamnonin suka ɗauka ta sha bamban da ta Atiku Abubakar mutumin da ya yiwa jam’iyar takara a zaɓen shekarar 2023 wanda yake kokarin samar da wata gamayyar jam’iyun adawa da za su tunkari APC a zaɓen 2027.

More from this stream

Recomended