Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta naɗa Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban ƙasa na dindindin na jam’iyyar.
Wannan naɗin ya biyo bayan taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 102 da jam’iyyar ta gudanar a ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025.
Tun da farko, Damagum ya jagoranci PDP a matsayin shugaban rikon kwarya, kafin yanzu da aka tabbatar da shi a matsayin shugaban dindindin na jam’iyyar.
Ana ganin wannan mataki zai taka rawa wajen ƙarfafa jam’iyyar yayin da ake ƙara shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
PDP Ta Naɗa Iliya Damagum a Matsayin Shugaban Ƙasa na Dindindin
