PDP ta naɗa Amina Arong a matsayin shugabar matan jam’iyar PDP

Jam’iyar PDP ta bayyana sunan, Amina Arong a matsayin sabuwar shugaban matan jam’iyar ta ƙasa..

Debo Ologunagba mai magana da yawun jam’iyar PDP shi ne ya sanar da naɗin, Arong a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Arong za ta kammala wa’adin tsohuwar shugaban matar jam’iyar, Stellah Effa-Attoe wacce ta mutu a cikin watan Oktoban 2023 bayan gajeruwar rashin lafiya.

Arong ta fito ne daga jihar Kuros Ribas.

More from this stream

Recomended