PDP 2019 – Atiku ne zai kara da Buhari a 2019

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a matsayin wanda zai kalubalanci shugaban Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a zaben da za a yi a watan Fabrairun 2019.

Alhaji Atiku Abubakar, ya samu takarar ne bayan ya samu nasara a kan abokan takararsa 11 wanda suma suka tsaya neman kujerar shugabancin Najeriyar a PDP.

Dan takarar shugabancin jam’iyyar na PDP, ya samu nasara ne da kuri’u 1532.

An dai gudanar da zaben ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers inda wakilai da dama daga jihohin Najeriya 36 suka hallara domin zabar dan takarar da zai yi gogayya da shugaba Muhammadu Buhari.

Sauran ‘yan takarar da suka nemi kejarar shugabancin Najeriyar a jam’iyyar PDP, sun hadar da:

  • Jonah Jang da ya samu kuri’u 19
  • Datti Baba ya samu kuri’u 5
  • David Mark kuri’u 35
  • Turaki Taminu kuri’u 65
  • Sule Lamido kuri’u 96
  • Bafarawa kuri’u 48
  • Dankwabo 111
  • Ahmed Markafi kuri’u 74
  • Kwankwaso kuri’u 158
  • Olubukola Saraki kuri’u 317
  • Aminu Tambuwal kuri’u 693

Jam’iyyun siyasar ta Najeriya, sun kammala zaben ‘yan takararsu ne a yayin da a ranar Lahadin nan ne wa’adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta ba jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takara ke cika.

More from this stream

Recomended