Paul Pogba ‘zai koma Juventus, Bayern Munich za ta ɗauko Sancho’

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wakilin Paul Pogba Mino Raiola ya soma tattaunawa da Juventus a kan komawar dan wasan kungiyar a bazara, amma Real Madrid da Juventus dukka suna sha’awar dauko dan wasan na Manchester United mai shekara 27. (Le10sport – in French)

Bayern Munich za ta iya yi wa kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer kafar-ungulu a yunkurin da yake yi na dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Sun)

Barcelona ta shirya sayar da dukkan ‘yan wasanta in ban da guda shida a bazara a yayin da kungiyar take fama da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon annobar korona. (Marca)

Wakilin Sergio Aguero ya yi watsi da rahotannin da ke cewa dan wasan na Manchester City mai shekara 31 zai iya barin Etihad a bazara, inda ake rade radin zai koma Argentina. (Mirror)

Dan wasanChelsea Willian, mai shekara 31, ya ce matakin da kungiyar ta dauka na ƙin sabunta kwangilarsa zuwa shekara uku da ke tafe ya jefa shi a cikin “mawuyacin” hali. (Esporte Interativo via Metro)

Manchester United ce a kan gaba a cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan Napoli Kalidou Koulibaly, mai shekara 28, bayan Paris St-Germain, Barcelona da Real Madrid sun fasa dauko dan wasan. (Sun)

Kazalika Manchester Unitedta tattauna da wakilin dan wasanJuventus mai shekara 25 Adrien Rabiot, a yayin da su ma Arsenal daEverton suke sha’awar dauko dan wasan. (Mirror)

Arsenal tana son dauko dan wasan Ajax da za a sayar a kan £20m Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, bayan dan wasan na Argentina ya murza leda a kungiyar a wasan kusa da karshe na Gasar Zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce. (Mirror)

Aana sa ran dan wasan tsakiya na Arsenal Ainsley Maitland-Niles, mai shekara 22, zai bar kungiyar idan aka bude kasuwar musayar ‘yan kwallon kafa a bazara bayan sun ɓaɓe da da sabon kocin kungiyar Mikel Arteta. (Star)

Real Madrid na duba yiwuwar bayar da mamaki a bazara inda za ta dauko dan wasan Celtic dan kasar Norway Kristoffer Ajer, mai shekara 22, bayan ya taka rawar gani a Gasar Premier ta Scotland. (Mundo Deportivo – in Spanish)

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...