Tsohon ministan sadarwa, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari a gidansa dake Daura.
Tsohon ministan ya bayyana ziyarar ne cikin wani sako da ya wallafa a kafafen sadarwar zamani.
“A yau na ziyarci babanmu His Excellency Muhammadu Buhari GCFR a garin Daura, jihar Katsina. Lalle maganganun dattawa maganganu ne na hikima. Muna rokon Allah Ya kara mana shiriya.” Pantami ya ce.
Babu wata sanarwa daga bangaren tsohon shugaban kasar kan dalilin ganawar mutanen biyu.