Oyarzabal ne gwarzon La Liga na watan Oktoba

Mikel Oyarzabal

An bayyana kyaftin din Real Sociedad, Mikel Oyarzabal a matsayin gwarzon gasar La Liga na watan Oktoba.

Mai shekara 23 ya taka rawar gani a Real Sociedad wacce ta dare mataki na daya a teburin La Liga na bana, wacce ta lashe wasa uku daga ukun da ta yi a watan.

A kuma lokacin kungiyar ta zura kwalo 10 a raga, inda daya ne ya shiga ragarta a watan na Oktoba.

Kyaftin din na Real Sociedad bai tsaya a matakin kashin bayan kungiyar ba kadai, shi ne kan gaba a cin kwallaye a Gasar La Liga ta bana.

Dan wasan ya ci kwallo biyar a gasar bana, inda ya zura uku a watan na Oktoba.

Real Sociedad tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 20 bayan karawa tara.

Kungiyar ta ci wasa shida da canjaras biyu da rashin nasara daya, ta kuma ci kwallo 20 aka zura mata hudu a raga.

Ranar 22 ga watan Nuwamba Real Sociedad za ta ziyarci Cadiz a wasan mako na 10 a gasar ta La Liga.

More from this stream

Recomended