Kotun da’ar ma’aikata ta zartar wa Mai shari’a Walter Onnoghen hukunci bayan karar da gwamnatin Najeriya ta shigar na zarginsa da kin bayyana kadarorinsa.
Kotun ta tsige shi daga mukaminsa kuma ta saka masa takunkumin hana shi rike mukamin gwamnati na shekaru goma tare da kwace kudaden da ke asusun ajiyarsa na banki inda gwamnatin ta mayar da su mallakarta.
A kwanakin baya ne gwamnatin kasar ta bukaci dakatacen alkalin alkalan kasar mai sharia Walter Onnoghen ya dakatar da aikinsa kan zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka inda ta gurfanar da shi gaban kotun da’ar ma’aikata.
Sai dai Onnoghen din ya daukaka kara inda ya kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu inda kotun ta yi watsi da kararsa daga baya.
Dakatar da Onnoghen a can baya ya jawo cece-kuce da dama a Najeriya inda har aka samu kungiyar lauyoyin kasar dai ta yi zanga-zanga kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka kan Mista Onnoghen inda ta bukaci mambobinta da su kauracewa kotu tsawon kwana biyu daga ranar Litinin.
Haka kuma a lokaci dakatarwar, babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma tarayyar turai sun yi allawadai da dakatar da shi.
Shugaba Buhari dai ya dakatar da Mista Onnoghen ne bisa shawarar kotun da’ar ma’aikata wacce ta samu alkalin alkalan da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi kan mukamin a 2017.