Ondo: Hukuma ta kama manoman ganyen tabar wiwi

Ma’aikatan hukumar NDLEA mai yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi sun samu nasarar kama wasu mutane hudu a jihar Ondo da ake zargi da noman ganyen tabar wiwi.

Jami’an hukumar ta NDLEA sun samu nasarar kama mutanen ne a gonarsu lokacin da suke tsaka da girbin ganyen tabar da aka haramta nomansa.

Mutanen da suka shiga hannun hukumar sun hada da Friday Azum mai shekaru 30,Friday Umuvole mai shekaru 26,Uba Avanum da kuma John Akor.

A cewar kwamandan hukumar na jihar Ondo,Haruna Gagara an kama mutanen da ganyen tabar wiwin da nauyinta yakai kiligiram 45.

Kwamandan ya ce yayin samamen jami’ansa sun samu nasarar lalata gonar tabar wiwin mai girma hekta 106.

More from this stream

Recomended