Omicron: Saudiyya ta dakatar da ƴan Najeriya shiga ƙasarta

[ad_1]

Saudiyya

Saudiyya ta dakatar da jiragen da ke shiga ƙasar daga Najeriya saboda ɓullar sabon nau’in cutar korona na Omicron.

BBC ta ga sanarwar da hukumomin Saudiyyan suka fitar a ranar Laraba, sannan wasu kamfanonin hada-hadar jiragen sama a Najeriyar ma sun tabbatar da hakan.

Wannan mataki da Saudiyya ta ɗauka ya sa ta zama ƙasa ta uku a baya-bayan nan da ta hana jirage daga Najeriya shiga ƙasashensu, baya ga Canada da Birtaniya.

Sanarwar ta ce: “Mun dakatar da shigar jirage ƙasarmu daga Najeriya, kuma mun dakatar da shigar duk wani ɗan Najeriya Suadiyya walau kai tsaye ko kuma ta hanyar yada gajeren zango a wata ƙasar.

“Sai dai za a ɗaga ƙafa ne kawai ga waɗanda suka yada zango na tsawon kwana 14 a wata ƙasar bayan fitarsu daga Najeriya, sannan ne za a iya barin su shiga Saudiyya,” in ji sanarwar.

Kazalika sanarwar ta ce ga ƴan Saudiyyan kuma daga suka shiga ƙasar daga Najeriya, to sai sun yi zaman killacewa na kwana biyar ko da kuwa suna da shaidar kammala riga-kafi.

Tun bayan da Saudiyya ta ɗage takunkumin shigar aikin Umara ƙasarta ne ƴan Najeriya suke ta rububin zuwa musamman a watan Oktoba da Nuwamba.

A ranar 16 ga watan Oktoban 2021 ne hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain, suka sanar da soke dokar bayar da tazara da aka tilasta a Masallacin Ka’aba a Makkah da kuma na Annabi a Madina.

Hakan kuma ya zo ne bayan ma’aikatar kula da harakokin cikin gida ta bayar da umarnin buɗe masallatan gaba ɗaya da kuma sasasauta matakan kariya da aka ɗauka.

Sai dai tun da farko hukumomin Saudiyya sun ce dole sai wanda ya kammala allurar rigakafin korona (guda biyu) ne zai iya shiga masallacin Makkah da Madina.

Tun da fari Saudiyya ta sassauta matakan korona ne bayan raguwar masu kamuwa da cutar a ƙasar.

An dakatar da yin Umrah a watan Maris din bara da rage yawan masu aikin Hajji tun ɓullar cutar korona kafin aka bude daga baya.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...