Ofishin Nuhu Ribadu Ya Musanta Zargin El-Rufai Na Biyan Fansa Ga ’Yan Bindiga

Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) ya musanta zargin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya ce gwamnati na biyan kuɗi ko bayar da wasu abubuwa ga ’yan bindiga domin samun zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin, Zakari Mijinyawa, ya fitar daren Lahadi, ONSA ta ce, “wannan zargi ba shi da tushe. Babu wani lokaci da ONSA ko wata hukuma a ƙarƙashin wannan gwamnatin ta shiga harkar biyan fansa ko ba wa masu laifi tallafi. Akasin haka, mun sha gargadin ’yan Najeriya da kada su biya fansa. Zargin El-Rufai ƙarya ne kuma ya saba wa hujjojin da ake iya gani a kasa.”

Sanarwar ta bayyana cewa tun daga farko gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki dabaru biyu a lokaci guda: gudanar da ayyukan soji da ƙarfin iko, tare da tattaunawa da al’umma domin magance ƙorafe-ƙorafen cikin gida.

A cewar ofishin da Nuhu Ribadu ke jagoranta, wannan tsari ya samar da sauƙi a wurare kamar Igabi, Birnin Gwari da Giwa a Jihar Kaduna, waɗanda a da suka sha fama da hare-haren ta’addanci amma yanzu suna samun ɗan zaman lafiya.

Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa an samu nasarori masu yawa wajen kamawa da kawar da manyan shugabannin ’yan bindiga a jihar. An bayyana cewa a Kaduna kaɗai, an hallaka ko kama shahararrun masu ta’addanci kamar Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari da Boka, tare da kama shugabannin kungiyar Ansaru da suka kafa sansanoni a yankin.

Sai dai sanarwar ta ce wannan nasara ta zo da asara, domin wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu a yayin fafatawa. “Don tsohon gwamna irin El-Rufai ya ƙaryata waɗannan sadaukarwa a kafar talabijin ta ƙasa, abin takaici ne kuma cin mutunci ga tunawa da jami’an tsaronmu,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, “muna kira ga El-Rufai da sauran ’yan siyasa da su guji ja da hukumomin tsaro cikin rikicin siyasa. Yaƙi da ’yan bindiga aiki ne na haɗin kai, ba dandalin neman maki na siyasa ba ne.”

More from this stream

Recomended