Obaseki: Me ya sa Shugaba Buhari ba ya iya ɗinke ɓarakar jam’iyyar APC?

0
Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Fadar shugaban kasar ta sha cewa Shugaba Buhari ba zai tsoma baki a rikice-rikicen siyasa ba

Matakin da gwamnan jihar Edo da ke kudancin Najeriya, Godwin Obaseki, ya dauka na fita daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar, bayan rikicin cikin gida ya ci tura tsakaninsa da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomole, ya sake fito da gazawar Shugaba Muhammadu Buhari ta magance rikicin jam’iyyar.

Rikici tsakanin Mista Oshiomhole – wanda tsohon gwamnan jihar ta Edo ne – da kuma mutumin da ya gaje shi, ya daɗe yana ruruwa, sai dai ya kai intaha ne bayan kwamitin da ke tantace ‘yan takarar gwamna ya hana shi damar sake tsayawa takara a jam’iyyar APC kafin zaben da za a yi nan gaba a wannan shekara.

Hakan ne ya sa ranar Talata ya garzaya fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ganawa da shi, da alama domin ya rarrashe shi ya sanya baki a rikicin.

Sai dai ga dukkan alamu ganawar ba ta yi armashi ba don kuwa bayan fitowarsa ne, ya bayyana wa manema labarai a fadar ta shugaban kasa da ke Abuja cewa ya fita daga APC kuma zai koma wata jam’iyyar don neman takara a wa’adin mulki na biyu.

Tun gabanin ganawar tasu, masu sharhi kan lamurran siyasa na ganin ba za ta sauya zane ba, saboda an sha kwatawa kuma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ga waɗanda a baya suka garzaya wurin shugaban kasar don ya sa baki a rikice-rikicen jam’iyyar ta APC a sassan kasar daban-daban.

Dr Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa ne kuma mai sharhi kan harkokinta daga Jami’ar Abuja ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewa Shugaba Buhari ba ya sanya baki a kan abin da ya shafi gidansa ma ballantana na jam’iyyar APC.

“Ba kasafai Shugaba Muhammadu Buhari yake sa baki a cikin rigingimu da husuma da ke faruwa ko da a jam’iyyarsa ta APC ko ma a cikin gidansa ba.

“Alal misali, a lokacin da rigingimu suka dabaibaiye tsohuwar jam’iyyarsa ta CPC a jihohi daban-daban musamman ma game da zabukan fid da gwani, bai ce komai ba har wadannan rigingimu suka yi wa jam’iyyar lahani kwarai da gaske.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK GOVT

Image caption

Sanata Rabiu Kwankwaso ya gana da Shugaba Buhari a Fadar shugaban kasa a watan Yuli na 2018

Kafin irin wannan rikicin ya dabaibaye Gwamna Obaseki, an yi wasu a baya, kamar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kuma duk da ziyarar da Sanata Kwankwaso ya kai wa Shugaba Buhari a wani yunƙuri na dinke barakar da ke tsakaninsa da Gwamna Ganduje, hakan bai yi tasiri ba, har Sanata Kwankaso ya fice daga APC zuwa PDP.

Lamarin da ya sa, jam’iyyar APC a zaɓen 2019 ta kusa rasa jihar Kano, inda Sanata Kwankwaso yake da ɗumbin goyon baya.

Kazalika bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin tsohon gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode da ubangidansa na siyasa Bola Ahmed Tinubu ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa, Mista Ambode ya ziyarci Shugaba Buhari inda ya nemi ya sanya baki.

Amma shi ma ƙarfi da yaji aka haramta masa sake tsayawa takara, saboda ganawar tasu da Shugaba Buhari ba ta sauya komai ba.

Haka ma fitaccen ɗan majalisar wakilan nan, Abdulmumini Jibrin, ya garzaya fadar shugaban kasar inda ya gana da Buhari, sakamakon rikicin siyasar da yake neman cin kujerarsa a wancan lokaci.

Ya je wurin shugaban kasar ne bayan jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kano ta hana shi sake tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai daga mazabar Kiru/Bebeji da ke jihar Kano.

Amma duk da ganawar da ya yi da shugaban kasar, jam’iyyar ta APC ba ta mara masa baya a zaben ba; hasalima wasu sun yi zargin cewa jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta goyi bayan dan takarar jam’iyyar PDP da ke hamayya a jihar.

Sai dai da ma fadar shugaban kasar ta sha cewa Shugaba Buhari ba mutum ne da ke son tsoma baki a rikice-rikicen jam’iyyarsa ba tana mai cewa ya fi so dimokradiyya a ko da yaushe ta yi halinta.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@AbdulAbmJ

Image caption

Jibrin ya gana da Shugaba Buhari lokacin da rikici yake neman cin kujerarsa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here