Obasanjo ya ƙaryata labarin mutuwarsa

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake cewa ya mutu.

Obasanjo ya bayyana haka ne a Osogbo  a yayin ƙaddamar da tsohon titin  Garage-Oke Fia da gwamnan jihar OsunAdemola Adeleke ya sake ginawa.

Ya ce akwai rahotannin mutuwarsa dake yawo a soshiyal midiya ya ƙara da cewa waɗanda suke so ya mutu su ne ke da hannu a yaɗa rahotannin.

“Na samu kira da sassafe daga wasu mutane inda su ka nemi na duba soshiyal midiya, ” Obasanjo ya faɗa sa harshen yarabanci.

“Nayi mamaki sosai da naga labarin dake iƙirarin na mutu da daddare. Na gaza gasgata labari.”

Tsohon shugaban ƙasar ya ce ya yi gaggawar sanar da iyalinsa da makusantansa labarin domin ya basu tabbacin yana cikin ƙoshin lafiya.

Ya ƙara da cewa “Waɗanda suke so na mutu fatansu kenan.Amma kuma Allah ya raya ni ina cigaba da rayuwa kuma waɗanda suke da wannan tunani a ransu ba za su tsira daga bala’i ba.”

More from this stream

Recomended