Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi suka mai tsanani ga gwamnatin Donald Trump yayin wani gagarumin taron yakin neman zaɓe da aka gudanar a jihohin Virginia da New Jersey.
Obama ya yi kira ga ‘yan Amurka da su nuna ƙarfinsu ta hanyar ƙin amincewa da abin da ya bayyana a matsayin rashin bin doka, sakaci, da hauka da ke faruwa a fadar White House.
A jawabin nasa, tsohon shugaban ya ce, Trump da wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar Republican na ƙoƙarin yaudarar jama’a ta yadda za su yi tunanin cewa gwamnati na aiki ne don ƙalilan, alhali kuma mafi yawan ‘yan ƙasa suna cikin wahala.
“Trump da ‘yan Republican na son su sa mutane su gaskata cewa wasu tsiraru ne kawai ke da muhimmanci a gwamnati, amma sauran jama’a su ci gaba da wahala,” in ji Obama.
Obama, wanda ba ya yawan tsoma baki a harkokin siyasa tun bayan saukarsa daga mulki, ya kuma gargadi ‘yan Republican kan gazawarsu wajen hana Shugaba Trump yin abubuwan da suka saba da doka da al’ada.
Ko da yake ba ya rike wani muƙami a yanzu, Barack Obama har yanzu yana da karbuwa sosai a tsakanin ‘yan jam’iyyar Democrat, kuma maganganunsa kan tasiri ne ga masu kada kuri’a a Amurka.
Obama Ya Caccaki Gwamnatin Shugaba Trump, Ya Gargadi ‘Yan Republican

