Shugaban Hukumar NYSC, Manjo Janar Olakunle Nafiu, ya bayyana cewa jihar Legas na adana kimanin naira biliyan 14.8 duk shekara ta hanyar amfani da matasan yi wa ƙasa hidima a fannoni daban-daban.
Ya faɗi haka ne a ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu a gidan gwamnati da ke Marina, inda ya bayyana cewa fiye da masu yi wa ƙasa hidima 44,000 ke aiki a jihar, ciki har da likitoci 303, malamai 7,148 da nas 274.
A cewarsa, idan jihar za ta ɗauki waɗannan ma’aikata aiki na dindindin, hakan zai ci kuɗi sosai. Ya kuma yabawa gwamnatin Legas saboda samar da yanayi mai aminci da ya sa jihar ta zama wuri mafi soyuwa ga masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya.
Gwamna Sanwo-Olu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa shirin NYSC, ciki har da gina sabon sansani a Ikorodu, tare da yaba rawar da matasan ke takawa a ilimi da kiwon lafiya.
NYSC Ta Ce Jihar Legas Na Adana Naira Biliyan 14.8 Duk Shekara Saboda Ƴan Bautar Ƙasa
