NUPENG Ta Janye Yajin Aiki Bayan Sasancin Da Aka Cimma Da Kamfanin Dangote

Kungiyar Ma’aikatan Mai da Gas (NUPENG) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a fadin kasa bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote Refinery and Petrochemicals.

Yajin aikin ya haddasa rufe gidajen mai da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Rikicin ya taso ne bayan zargin cewa kamfanin Dangote ya hana ma’aikatansa shiga ƙungiyoyin kwadago.

Taron sulhu da Ministan Kwadago, Muhammad Maigari Dingyadi ya jagoranta a Abuja ya haifar da sanya hannu kan yarjejeniya.

A cikin takardar yarjejeniyar an ce: “Tun da shiga ƙungiyar kwadago hakki ne bisa doka, hukumar Dangote Refinery and Petrochemicals ta amince ma’aikatan da suke so za su iya shiga ƙungiya. Za a kammala wannan tsari daga 9 zuwa 22 ga Satumba, 2025. Babu wani ma’aikaci da za a ci masa zarafi saboda yajin aikin.”

More from this stream

Recomended