NNPP Ta Yi Fatali Da Sakamakon Zaben Maye Gurbin a Kano

Jam’iyyar NNPP ta bayyana rashin amincewarta da sakamakon zaben maye gurbi na mazabar Tsanyawa/Ghari a Kano, inda aka bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa, ya ce, “manufar jam’iyya ita ce ta tunkari kotu saboda magudin da aka shirya domin hana ‘yan Kano ‘yancinsu.”

Ya kuma bayyana cewa, “duk da cewa an gudanar da zabe lafiya a rumfunan da kotu ta bayar da umarnin sake zabe, wasu ‘yan siyasa tare da jami’an INEC sun yi kutse suka tilasta bayyana dan takarar APC a matsayin mai nasara.”

Dungurawa ya kara da cewa, “jam’iyya za ta ci gaba da yakar rashin adalci, son zuciya da duk wani yunkurin amfani da karfin gwamnati wajen tauye hakkin al’ummar Kano.”

More from this stream

Recomended