Kamfanin mai na NNPCL ya sake ƙara kuɗin man fetur a gidajen mansa dake faɗin ƙasarnan.
Wannan ne karo na biyu da kamfanin yake ƙara kuɗin a cikin watan Oktoba.
Kamfanin na NNPCL ya ƙara farashin kuɗin litar man fetur daga farashin ₦855 da ya saka a watan Satumba ya zuwa ₦998 ranar 3 ga watan Oktoba..
Amma jaridar The Cable ta lura cewa wasu daga gidajen man kamfanin dake Lagos farashin man fetur ya ƙaru ya zuwa ₦1025 kowace lita.
A wani gidan man kamfanin dake yankin Kubwa a birnin tarayya Abuja ana sayar da kowace lita akan ₦1050.
Sauran gidajen mai na kamfanoni irinsu AA RANO, Mobil, Rainoil sun ƙara na su farashin a tsakanin ₦1100 ya zuwa ₦1250.
Ƙarin na zuwa ne sama da wata guda bayan da kamfanin man na NNPCL ya sanar da fara ɗaukar mai daga matatar man fetur ta Dangote.