NNPCL ya sake ƙarin kuɗin man fetur

Kamfanin mai na NNPCL ya sake ƙara kuɗin man fetur a gidajen mansa dake faɗin ƙasarnan.

Wannan ne karo na biyu da kamfanin yake ƙara kuɗin a cikin watan Oktoba.

Kamfanin na NNPCL ya ƙara farashin kuɗin litar  man fetur daga farashin ₦855 da ya saka a watan Satumba ya zuwa ₦998 ranar 3 ga watan Oktoba..

Amma jaridar The Cable ta lura cewa wasu daga gidajen man kamfanin dake Lagos farashin man fetur ya ƙaru ya zuwa ₦1025 kowace lita.

A wani gidan man kamfanin dake yankin Kubwa a birnin tarayya Abuja ana sayar da kowace lita akan ₦1050.

Sauran gidajen mai na kamfanoni irinsu AA RANO, Mobil, Rainoil sun ƙara na su farashin a tsakanin ₦1100 ya zuwa ₦1250.

Ƙarin na zuwa ne sama da wata guda bayan da kamfanin man na NNPCL ya sanar da fara ɗaukar mai daga matatar man fetur ta Dangote.

More from this stream

Recomended