
Babban Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL ya kara farashin man fetur daga N910 ya zuwa N945 a gidajen mansa dake Abuja.
Har ila yau kamfanin ya kuma kara farashin man a birnin Lagos daga naira N870 ya zuwa N915 kan kowace lita a gidajen mansa dake birnin Lagos.
Sabon karin farashin man fetur din na nufin karin N35 kan kowace lita a birnin Abuja a yayin da a Lagos karin ya zama N45 kan kowace lita.
A ziyarar da wakilin jaridar Daily Trust ya kai a daya daga cikin gidan man NNPCL dake Fin Niger a kan titin Lagos – Badagry ya tarar ana sayar man fetur din kan naira 915 kan kowace lita.
A birnin Abuja gidan man kamfanin na NNPCL dake Kubwa yankin Fedaral Housing an kara farashin daga naira 910 ya zuwa 945 kan kowace lita.
Sauran kamfanonin mai kamar su MRS ya kara kudin litar mai daga N875 kan kowace lita ya zuwa N925 a birnin Lagos.