Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL, ya sake rage farashin man fetur a ƙasar.
Rahotannin da manema labarai suka tattara a safiyar Litinin a Abuja sun nuna cewa gidajen mai na NNPCL sun saukar da farashin man fetur daga ₦835 zuwa ₦815 a kowace lita, wato an rage shi da ₦20.
An tabbatar da sabon farashin a wasu gidajen mai na NNPCL da ke Wuse Zone 4 da 6, hanyar Keffi–Abuja, da Kubwa Expressway.
Wani ma’aikacin gidan mai na NNPCL, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an fara aiwatar da sabon farashin tun yammacin Lahadi.
Sai dai duk da wannan ragi, farashin NNPCL na ₦815 har yanzu ya fi na wasu gidajen mai da Dangote Refinery ke tallafawa, musamman MRS, inda ake sayar da litar man fetur a ₦739 a faɗin ƙasar nan.
Za a iya tunawa cewa a ranar 19 ga Disamba, 2025, NNPCL ta rage farashin man fetur da ₦80, bayan fara gasar rage farashi tsakanin kamfanonin da ke harkar rarraba man fetur a ƙasar nan, wanda Dangote Refinery ta tayar bayan ta rage farashin man fetur zuwa ₦699 a matakin tasha (gantry).
NNPCL Ta Kara Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦815 A Kan Lita

