NNPCL Ta Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa N905 A Kan Kowace Lita

Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya ƙara farashin man fetur (Premium Motor Spirit) a wasu wuraren sayar da mai da yake da su a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa shagunan NNPCL da ke Wuse Zone 6 da Zone 4 sun ɗaga farashin man daga N890 zuwa N905 a kan lita, wanda ke nufin ƙarin N15 ko kusan kashi 1.7 cikin ɗari.

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Mai ta Ƙasa (IPMAN), Alhaji Abubakar Maigandi, ya danganta wannan ƙarin farashin da matsalar karancin isar da mai sakamakon takaddama tsakanin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (PENGASSAN) da kuma Kamfanin Man Dangote.

An tuna cewa takaddamar da ta ɓarke tsakanin PENGASSAN da Kamfanin Man Dangote ta samo asali ne daga korar wasu ma’aikatan Najeriya, lamarin da ya janyo yajin aikin tsawon kwanaki biyu.

Sai dai gwamnatin tarayya ta shiga tsakani, wanda hakan ya sa aka dakatar da yajin aikin bayan tattaunawa.

Wannan sabon ƙarin farashi ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwa ke ci gaba da kokawa kan tsadar sufuri da kayan masarufi a faɗin ƙasar.

More from this stream

Recomended