Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta bukaci a saki shugabanta Joe Ajaero ba tare da wani sharaɗi ba.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja biyo bayan wani taron gaggawa Abujaa majalisar gudanarwar kungiyar ta NLC ta nemi a sako shugaban kafin ƙarfe 12:00 na daren ranar Litinin.
A ranar Litinin ne mai magana da yawun kungiyar ta NLC, Benson Upah ya bayyana cewa jami’an tsaron DSS sun yi awon gaba da Ajaero a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja akan hanyarsa ta zuwa ƙasar Birtaniya halartar wani taro.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa an kama shugaban ne a ƙoƙarin rufe bakin kungiyar saboda kan yadda take nuna adawa da manufofin gwamnati.
A kwanakin baya ne shugaban na NLC ya amsa tambayoyi a hedkwatar rundunar ƴan sanda dake Abuja biyo bayan bisa wasu zarge-zarge da ake masa.