Nijeriya Ta Gurfanar da Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Fiye da 100 a Cikin Shekaru Biyu—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, Nijeriya ta gurfanar da fiye da 100 daga cikin masu daukar nauyin ta’addanci da kuma tallafawa kungiyoyin ta’addanci cikin shekaru biyu da suka gabata.

Tinubu, wanda sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya wakilta, ya bayyana wannan a Abuja a ranar Talata yayin taron da Hukumar Leken Asiri ta Nijeriya (NFIU) ta shirya, wanda ya tattara kungiyoyin yaki da masu daukar nauyin ta’addanci da kuma yaki da cin hanci da rashawa (AML/CFT/CPF).

Ya kara da cewa, “Mun samu ci gaba mai yawa wajen tunkarar barazanar ta’addanci da laifukan da ke tattare da shi, musamman ta hanyar matakan da jami’an tsaronmu suka dauka. A kokarinmu na yaki da masu tallafawa ‘yan ta’adda, ta hannun ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da babban lauyan gwamnatin tarayya, mun gano kuma mun gurfanar da sama da 100 cikin shekaru biyu da suka gabata.

“Ta hanyar dakatar da hanyoyin samun kuɗi da kayan aiki, mun hana Boko Haram da ISWAP gudanar da hare-haren ta’addanci a kan al’ummominmu da ‘yan kasa.”

More from this stream

Recomended