Nijeriya Ka Iya Shiga Duhu A Sakamakon Lalacewar Injinan Samar Da Wutar Lantarki – GENCoc

[ad_1]








Gamayyar kamfanonin da ke samarwa da raba wutar lantarki a Nijeriya (GENCos) sun gargadi hukumomin kasar game da yiwuwar shiga matsalar samun wutar lantarki.

A wata sanarwa da babban sakatariyar daya daga cikin kungiyoyin da ke cikin gamayyar, APGC, Joy Ogaji ta aikawa manema labarai a jiya Alhamis, ta bayyana cewa gaba daya injinan samar da wutarsu na ta haska danjojin da ke nuna cewa a kowane lokaci za su iya daina aiki.

Ta ce wannan abu na faruwa ne saboda Kamfanin Raba Wuta na Nijeriya, TCN, ya kasa jan adadin wutar da ya kamata ya ja ya kai cikin tashar tattara wutar lankarki ta kasa, wato National grid.

Ta ce ko a watan Afrilu, an samu karfin wuta kimanin megawat 7,485, amma TCN 3985 kawai ta iya zuka ta raba.

Wannan dalilin ne ya sa injinan ke fuskantar matsala. A cewar Ogoji injinan kamar kayan wuta suke, idan wuta ta yi musu kadan, ba za su iya aiki ba. Idan kuma ta yi musu yawa, za su lalace.




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...