Nigeria@60: Waiwaye kan tarihin Yarbawa bayan shekara 60 da samun Æ´ancin Najeriya

Wannan maƙala ce ta musamman da BBC ta rubuta albarkacin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ƴancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Burtaniya.

Za mu kawo tarihi na manyan ƙabilun ƙasar uku da suka haɗa da Hausawa da Yarabawa da Igbo cikin kwana uku a jere.

A ci gaba da kawo muku tarihin manyan kabilun Najeriya albarkacin cikar kasar shekara 60 da samun ‘yancin kai, yau za mu yi duba kan kabilar Yarabawa wanda daya ce daga cikin manyan kabilu mafi yawan jama’a a Najeriya.

Su wane ne Yarabawa?

Masana harkokin al’adu da na cewa duk da gauraya al’adu irin na zamani amma ba su sanya Æ™abilar Yarbawa sun yi watsi da al’adunsu da suka gada tun iyaye da kakanni ba.

To sai dai da yawa daga ‘yan wannan Æ™abila na cewa tsatsonsu sun fito daga wani mutum da ake kira Oduduwa har zuwa lokacin da ya kafa gari da a yanzu ake kira Ile-Ife – sai dai wasu daga cikinsu na ja da cewa Oduduwa shi ne mafarin tarihinsu.

Da yawa daga kabilar Yarbawa sun yi imani cewa tarihinsu ya faro daga fitaccen jarumi da ake kira Oduduwa wanda kuma garin Ile-Ife ke a mazauni farkon matsugunninsu.

Kuma har kwanan gobe ana yi wa Oduduwa ganin jajirtaccen bil’adama kuma fitila ga sayensu haske kuma ga tafarkin kabilar Yarbawa.

Yarbawa dai na da É—umbin kayayyakin tarihi da al’adu, suna da Obatala wanda ke a matsayin ubangijinsu.

To sai dai sakamakon wanzuwar addinin Musulunci da Kiristanci da wayewa ko bakin al’adu daga Turai, an samu raguwar kamanta Allah da wani abu da kuma tsagwaron al’adunsu na gargajiya.

Oduduwa kamar yadda masana tarihi suka nuna na cewa Lamaruzu shine mahaifin Oduduwa – ya fito daga kasashen gabas- har ma ake yi masa kirari da cewa Lamaruzu na yamma da Makka. Ya karaso Ile-Ife da jama’arsa wajajen karni na hudu.

Cikin Kabilar Yarbawa akwai wadanda suka yi imani cewa Oduduwa mutum ne, wasu kuwa na cewa ba shine tushen wannan kabila ba. Sai dai har kwanan gobe ana yi masa kallon uban ko mafarin duk wani da ya fito daga ƙabilar Yarbawa.

Basarake Oba Hammed Adekunle Makama, shi ne sarkin garin Olowu-Kuta mai daraja ta daya a jihar Osun, haka nan kuma tsatso ne daga zuria’r Oduduwa.

Oba Hammed Adekunle

Bayanan bidiyo,
Muna cikin jikokin Oduduwa na fari

Ya ce “an yarda cewa oduduwa shi ne magabatan Yarbawa. To amma kamar yadda ake cewa ya sauko daga sama da sarka, maganar gaskiya baki bai zo daya ba.

To amma kasar Yarbawa akwai wadanda ba su yarda da cewa Oduduwa shi ne magabacin Yarbawa ba kamar Sarki Atta na Ijebu-Ode ya ce babu abin da ya hada su da Oduduwa.

Wasu sun ce Oduduwa ya fito daga gabas ta hanyar Yamai ta Jamhuriyar Nijar, yana tafiye-tafiye har ya zo Ile-Ife.”

Kabilar Yarbawa suna da jiga-jigan sarakuna kamar su Ooni na Ife da Alaafin na Oyo da Olubadan na Ibadan.

Wadannan su ne rukunan sarakuna masu daraja ta daya. Ko da yake akwai wasu daga cikinsu da ke da makamanciyar wannan sarauta amma kuma darajarsu ta bambanta.

Oba Hameed ya kara da cewa “Muna da wata al’ada ta gaisuwa wacce muke kira Do’baale, wanda mutum zai yi ruf da ciki ya mike ya yi gaisuwa a gaban sarki, wannan al’ada ce mai ban sha’awa.

”Mu a kasar Yarbawa yadda muke jaddada al’adunmu daban suke da na arewa. Na arewacin Najeriya addini ya fi yawa; to amma ga Yarabawa addini daban haka kuma al’ada daban. Al’adarmu ta bakaken fata daban take da ta Larabawa.”

”In ba mu yi kokari ba, anan gaba duk tushenmu ma sai mun zo mun manta da su. Mu a kudu in ka ga an naÉ—aka kan sarauta to ana yi ne domin mu raya da jaddada al’adunmu ne,” in ji shi.

Al’adun Yarbawa

Yarbawa sun yi fice ta fuskar raya al’adu kamar a lokacin biki ko suna ko a sa’ilin auratayya har ma da rabon gado.

Al’adarsu ta auratayya na zuwa da biyan sadaki- to amma kuma in namiji ko saurayi ya ga budurwar da yake so, to a maimakon ya fada mata kai tsaye’ sai ya je ya fada wa iyayensa domin a yi masa iso gun iyayen budurwa.

Akasari iyaye na bayar da gudunmowa game da wadanda ‘ya’yansu za su aura.

Dalilin haka kuwa ya zo domin kauce haduwa da miyagun Æ™addarori kamar na ciwon hauka ko wasu cututtuka ko tsinuwa da mai yiwuwa akwai su a cikin zuri’ar matashin ko budurwar da yake so ya aura.

Ana raye-raye da ruguntsumin raya al’adu bilhakki.. Sai dai a yanzu ana gauraya su da wasu tsare-tsare da zamani ya zo da su.

Sun nuna shi kansa addini wani É“angare ne daga cikin al’adunsu – saboda haka ake la’akari da fifita al’adu kuma suke ci gaba da tasiri cikin al’amuransu na yau da kullum.

Sai dai kuma ana samun sauyi nan da can sakamakon shigowar addinin Musulunci da na Kirista da kuma shigowar Turawan mulkin mallaka a yankunansu.

Daga ina Oduduwa ya fito?

Masana tarihi kamar Dr. Muhammad Musa Maitokobi ya ce, kamar yadda bincike ya nuna Oduduwa ya fito daga kasashen gabashi ne- sai dai ana tankiya cewa ba za yi garajen cewa wannan kasa ko waccar ba.

Wasu alkaluma na tarihi na nuni da cewa akwai alaka mai karfi ta al’ada a tsakanin kabilar Yarbawa da Barebari musamman kan wasu al’adu da suke kamanceceniya.

“Domin kuwa shi Lamaruzu wanda shi ne uban Oduduwa, ya fito daga kasashen gabas ne – tarihi ya nuna tare suke da Barebari- wannan ne ya sa ake yi masa kirari cewa Lamuruzu na yamma da Makka.

”Hakanan kuma akwai al’adu da yawa wadanda sun yi dai-dai da al’adunsu wadanda kabilun biyu suke da kamanceceniya kamar ‘hatta Gunda da ake maganarta ta bangaren Barebari, Yarbawa ma suna da ita.

”Akwai wani Girke na ganguna irin nasu wadanda ake kakkafasu a kasa, duk suna da irinsu.

”Suna da son juna da rashin kar na gaza, kar kuma mu bari dan uwanmu ya gaza sun tafi iri daya. Akwai wata rijiya a nan cikin gidan sarautar Ile-Ife; tana nan da akwai sarka.

”A sani na irin wannan rijiyar akwai ta a wani kauye da ake kira Gazargamu a tsakanin Bultuwa da Subdu -da Galdiram inda yake mai tarihi.

To ina ce yamma da Makka, yamma da Makka gabadaya dai tun daga Maiduguri yamma da Makka ne,” in ji Dr Maitakobi.

Malam Abdulkabir Bayerabe ne, ya ce duk da addinin Musulunci da na Kirista sun ratsa kabilar Yarbawa, to amma har kwanan gobe ba su yi watsi da al’adunsu É—ungurungum ba.

”Har yanzu muna gudanar da wasu al’adunmu na gargajiya; yanzu wannan gari da kake gani na Ile-Ife sun yi amanna cewa daga can ne hasken duniya yake fitowa.

In suna bikinsu na al’ada za ka ga sun É—auko wani mayafi fari ko harami su yafa, amma ba saboda addini ba sai domin tsafe-tsafe da sauran al’adunsu.

Hakanan idan ana so a tsinewa mutum ana yi masa barazana da cewa za a fada wa Oduduwa ya la’ance shi- kamar ga Bayerabe domin mutum ya kiyaye.

Idan Oduduwa ya tsine maka tsinuwar za ta tabbata. To amma har yanzu akwai sauran al’adun namu sai dai ba su da karfi- sakamakon shigowar addinin Musulunci da kuma Kiristanci da kuma shigowar bakin al’adu na Turawa.

Al’adun mutuwa

Abinda ya shafi kide-kide da rawa na Yarbawa har kwanan gobe ana yi ba a bar su ba. WaÉ—annan ba a fitar da su daga cikin al’adu ba.

Yanzu misali a abinda ya shafi mutuwa a jihohin Ekiti da Ondo a kan ajiye gawa domin a yi mata biki- to amma kamar anan Osun musamman a yankunan da Musulunci ya yi Æ™arfi, ba mu yarda da wannan al’ada ba.”

Ita kuwa wannan malama mai suna Mrs. Busola ta ce al’adunsu da suka shafi abinci da sauransu suna cikin abubuwan da suke alfahari da aka haifesu cikin Æ™abilar Yarbawa.

”Yarbawa mutane ne da ke biyayya ga manyansu da marabtar baÆ™i da kuma nuna kulawa ga jama’a. Muna mu’amala da wasu Æ™abilu da kuma mabiya addinai daban-daban.

”Addininmu na gargajiya suna nuna allolinmu na baiwa kamar Ogun da Sango da Osun da Obatalamo da sauransu. Eh! Ina godiya ga Oludumare da ya halicce ni Bayarbiya.

”Matanmu suna sanya tufafin Iro da buba tare da gele, yayin da mazajenmu kan sanya kayan saki kamar hula da buba da shokoto.

”Ni Bayarbiya ce, kuma ina alfahari da al’adata. Al’adun Yarbawa suna da ban sha’awa wadanda suke nuna asalinmu wanda shi ne garin Ile-Ife.

”Kuma abincinmu kamar Iyo da dakakkiyar sakwara da Amala da Eba waÉ—anda ake yin su da rogo suna kwadaita min cinsu da samun nishadi,” in ji Mrs Busola.

Wasu al’adu da wannan Æ™abila ta yi fice a kansu sun haÉ—a da doba’le da akan yi ruf da ciki a fadi a gaban sarki domin yin gaisuwa a gaban sarki; a yayin da mata kuwa kan tsaya bisa gwiwowinsu a kasa sa’annan su gaishe da Basarake.

Abincin Yarbawa

A kasar Yarbawa ma dai ana samun Oloyes kwatankwacin fadawan sarki da ake samu a masarautun da ke arewacin Naijeriya. Abincin da aka fi saninsu da shi dai sun hada teba da suke kira E’ba da doya da kuma .

Yarbawa suna noma kan wadannan cimaka, sai dai mafi yawa su ne ‘ya’yan itace- kuma akwai mafarauta a cikinsu.

A baya ana samun magidanci na aurarraki da yawa, sai dai kuma abinda addini ya zo da shi da kuma zuwan Turawan mulkin mallka a sannu-sannu an yi watsi da wasu daga cikinsu.

Game da haihuwa kuwa duk yaron da yake shi ne dan fari akan kirashi da Dawodu a yayin da ‘ya mace ake kira ta da Bee’re.

KaÉ—e-kaÉ—en Yarbawa

KaÉ—e-kaÉ—e da kuma imani da magungunan gargajiya har kwanan gobe suna yin tasiri cikin rayuwarsu. Malam AbdulKabir wanda Bayerabe ne ya gasgata fifita al’ada a wannan shiyya.

Yara daga wannan Æ™abila dai ana ba su tarihin Oduduwa, wani mahaluki ne cikakken jarumi da ya gagari maza da dauloli. Wanda da haka ake cusawa yara koyon al’adu da tsayawa a kansu.

Malam Abdulkabir ya ce sun san da haka a lokacin da suke ƙanana.

(BBC Hausa)

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...