Nigeria Ta Kebe N1.7tr Domin Shirin Ci Gaban Kasa PEWASH.

[ad_1]

Shirin na Gwamnatin Tarayya mai taken PEWASH dake mayar da hankali wajen samar da ruwa, tsabtar muhalli da na jiki, da ma’aikatar ruwa ta Najeriya ke jagoranta, na da zummar cimma “dawwamammun muradun Karni” masu dorewa da ake kira [SUSTAINABLE DEVELOPMENT GOALS], da turanci. Shirin da tuni gwamnatin tarayya ta kebe wa Naira Triliyan daya da Milyan dari bakwai don tabbatar da nasararsa.

Jihar Kano ce ta biyu a Tarayyar Nigeria wajen rungumar shirin gadan gadan, inda gwamnatin jihar ta sanya hannu bisa yarjejeniyar aiki tare da ma’aikatar ruwa ta kasa. Gwamnan jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa Muryar Amurka Muhimmancin shirin a garesu inda ya ce ”Muhimmancinsa yana da yawa kwarai da gaske, tunda in an yi maganar ruwan sha ai an yi maganar rayuwa kenan, kuma in an yi maganar tsabtace muhalli da kuma kula da lafiya, wadannan ababe in ka hadasu to kaga abin da mutane suke bukata kenan, musamman in kasan irin abubuwan da suke faruwa a kauyukanmu to za ka san cewa wannan tsari da aka dauko,tsari ne da zai kyautata rayuwa a Nigeria musammanma mu a nan arewa””

A baya dai shirin cimma muradun karni da ake kira MDGs a takaice, bai sami cikakkiyar nasara ba a Nigeria, kuma gashi yanzu an dora da ci gaban shirin wato shirin ci gaba mai dorewa na SDGs, ko me ya kawo tarnaki a shirin farko na MDGs din? Ministan albarkatun ruwa na Nigeria Injiniya Sulymanu Hussaini Adamu, ya ce batu ne na kasafin kudi, abin kenan da ya sa gwamnatin tarayya da na jihohi suka fito da wani tsari na zayyana irin rawar da kowane bangare zai taka,

Misali inji Minista Sulayman Adamu,an daddale abin da gwamnatin Tarayya za ta yi da kuma wanda gwamnatin jiha za ta yi.Idan gwamnatin jiha taki sauke nauyin da ke kanta sai gwamnatin Tarayya ma ta noke. Yaci gaba da cewa an yi hakan ne da nufin ganin ba a sami matsalar da aka samu ba a baya. A naso ne don a kara zumma akan abin a taimakawa mutane dangane da batun harkar ruwan sha.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin karin bayani

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...