Niger na so a gasa naman sallah da gawayi

[ad_1]

Rago

Hakkin mallakar hoto
Anadolu/Getty Images

Image caption

An fi amfani da raguna wajen yin layya a lokacin sallah babba

An bukaci mutane a jamhuriyyar Nijar da su rage amfani da itace a lokacin bukukuwan sallah babba a kasar.

A lokacin sallar ne iyalai kan yanka ragon layya su gasa shi kafin su ci.

A Yamai, babban birnin kasar, akalla ana kona kashi daya bisa biyar na itacen da ake konawa a shekara, a lokacin sallar kadai.

Sare itatuwa na da alaka da kwararar hamada, matsalar kuma da kasar ta kwashe shekaru tana fama da ita.

A lokacin bikin sallar da ake yi wa lakabi da “Tabaski”, hukumomi na sa ran za a yanka raguna kusan 400,000 a birnin na Yamai kadai.

Kuma a wajen gasa ragunan za a yi amfani da kusan tan 50,000 na itace.


Muhimmancin sallar layya

Hakkin mallakar hoto
AFP

  • Ranar sallah babba rana ce ta hutu a kasashen Musulmi.
  • A lokacin bukukuwan sallah, ga wanda ke da hali, Musulmi a fadin duniya na yanka raguna, wasu kuma tumaki domin yin koyi da Annabi Ibrahim Alaihim Salam wajen bin umarnin Allah (SWT) da ya yi.
  • Musulmi da Kirista da Yahudawa sun yi imanin cewa Allah SWT ya umarci Annabi Ibrahim (Abraham) a cikin mafarki da ya yanka dansa Annabi Ishaqa (Isaac).
  • Sai dai Shaidan ya yi kokarin hana Annabi Ibrahim bin umarnin Allah (SWT) inda ya nemi kada ya kashe dansa.
  • Kafin Annabi Ibrahim ya yanka dansa, sai Allah ya musanya shi da rago.
  • Iyalai na rarraba naman layya ga wasu iyalan da abokan arziki da ma wadanda basu da galihu, inda ake baiwa kowannensu kashi daya bisa uku na naman.
  • A ranar Idi Musulmi na fara zuwa masallaci ne domin yin sallar Idi, suna sanya kaya masu kyau tare da gode wa Allah (SWT) a kan ni’imomin da ya yi musu.
  • Haka kuma a kan kai ziyara ga ‘yan uwa da abokan arziki tare da raba kyaututtuka.

Ku yi amfani da gawayi

Shugaban hukumar da ke kula da muhalli na Yamai, Kanal Oumarou Alou, ya yi kira ga mutane da su yi amfani da gawayi maimakon itace, don jami’ai za su hana motoci da jakuna da kuma rakuma daukar itace zuwa cikin birnin don rage yawan itacen da ake amfani da shi.

“Muna duba hanyoyin da zamu rage yawan itacen da ake amfani da shi tare da duba wasu hanyoyin da za a samar da wutar girki da karfe ko kuma da gawayi. Ya shaida wa BBC Afrique hakan.

“Muna kokarin yada sakon ga kungiyoyi masu karfin fada a ji, don mu kare dazuzzukanmu.”

Nijar na daya daga cikin kasashe matalauta a duniya, kuma kasa ce da ke daura da Hamadar Sahara.

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...