An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle.
Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta sanar da naɗin na Finidi a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Finidi mai shekaru 52 zai maye gurbin Jose Poseiro wanda ya yiwa mataimaki na tsawon watanni 20.
Poseiro ya ajiye aikinsa ne a cikin watan Faburairu bayan da ya jagoranci tawagar ta Super Eagle ya zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Nahiyar Afirka da aka yi a ƙasar Kodebuwa.
Kafin tabbatar da shi Finidi ya kasance mai horar da kungiyar na riƙon ƙwarya inda ya jagoranci tawagar kungiyar a wasan sada zumunci guda biyu da suka buga da ƙasar Ghana da kuma Mali.