Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale a ƙasar Chad.
A wata sanarwa ranar Laraba hukumar ta ce ƴan Najeriyar da aka dawo da su sun haɗa da yara 71 mata 48 jarirai 8 da kuma maza 23..
Hukumar ta ce waɗanda aka dawo da su sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos ranar Talata 08:30 na dare.
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ita ce ta taimaka wajen kwaso mutanen.
Jirgin saman kamfanin Air Cargo mai rijistar namba SU-BUR shi ne ya sauke mutanen a filin jirgin saman na Murtala Muhammad dake Ikeja da ƙarfe 08:30 na dare.
Wasu daga cikin mutanen sun bayyana jin daɗinsu kan nasarar da aka samu ta dawo da su gida lafiya.