NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale a ƙasar Chad.

A wata sanarwa ranar Laraba hukumar ta ce ƴan Najeriyar da aka dawo da su sun haɗa da yara 71 mata 48  jarirai 8 da kuma maza  23..

Hukumar ta ce waɗanda aka dawo da su sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos ranar Talata 08:30 na dare.

Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ita ce ta taimaka wajen kwaso mutanen.

Jirgin saman kamfanin Air Cargo mai  rijistar namba SU-BUR shi ne ya sauke mutanen a filin jirgin saman na Murtala Muhammad dake Ikeja da ƙarfe 08:30 na dare.

Wasu daga cikin mutanen sun bayyana jin daɗinsu kan nasarar da aka samu ta dawo da su gida lafiya.

More from this stream

Recomended