Ndume yaƙi komawa sabon ofishinsa

Sanata mai wakiltar mazaɓar kudancin jihar Borno a majalisar dattawa sanata Ali Ndume ya ƙi karbar sabon ofishin da kwamitin ayyukan majalisar dattawa ya bashi a cikin ginin majalisar dattawa.

A cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaban kwamitin ayyukan majalisar dattawa a ranar Talata, Ndume ya ce ginin ofishin da aka bashi bai dace da girma da kuma matsayinsa ba a majalisar.

Takardar ta ce Ndume ya ƙi karbar ofishin ne saboda tun da farko ana duba ɗaɗewar sanata a majalisar sannan a bashi ofishi.

“Sanata Ndume shi ne sanata mafi daɗewa a majalisar dattawa bayan sanata Ahmed Lawan saboda haka za a bashi ofishine kaɗai a hawa na huɗu,”  a cewar takardar.

A ƴan kwanakin da suka wuce ne aka sauke Ndume daga muƙaminsa na bulaliyar majalisar bayan da ya soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu.

More from this stream

Recomended