NDLEA Ta Kama ’Yar Brazil Da Hodar Iblis Ta Naira Biliyan Uku A Filin Jirgin Abuja

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta sanar da kama wata ’yar kasar Brazil mai shekaru 30, Ingrid Rosa Benevides, a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

NDLEA ta ce an kama matar ne bayan ta shigo Najeriya dauke da kilo 30.09 na hodar iblis farin launi da aka boye a cikin fakitin kofi da aka kullerun daga kamfani, wadda kimarta a kasuwa ta haura Naira biliyan uku.

Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kama wacce ake zargin ne a ranar Juma’a bayan saukarta daga jirgin Qatar Airways mai lamba QR1431, sakamakon sahihan bayanan sirri da aka samu a kanta.

Bincike da aka yi wa jakunkunanta biyu ya gano fakitin kofi 21, amma bayan budewa sai aka tarar da hodar iblis maimakon kofi. Hukumar ta ce wannan ita ce mafi girman hodar iblis da aka taba kamawa a filin jirgin Abuja.

A cewar NDLEA, wacce ake zargin ta bayyana cewa ta shigo Najeriya ne a matsayin mai hutu, alhali tana dauke da miyagun kwayoyi.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta samu nasarar kama wasu mutane da dama da kuma kwato miyagun kwayoyi a jihohi daban-daban ciki har da Lagos, Kano, Kaduna, Borno, Ekiti, Edo da Benue, a wani bangare na yaki da fataucin miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yabawa jami’an hukumar bisa kokarinsu, tare da bukatar su ci gaba da aiki cikin kwarewa da gaskiya wajen dakile safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

More from this stream

Recomended