Jami’an hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi sun kama, Adrienne Munju wata ƴar ƙasar Kanada da ta shigo da wata nau’in ganyen yanar wiwi da ake ƙirƙirar a ɗakin binciken kimiya.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya ce matar mai shekaru 41 an kama ta ne ranar 03 ga watan Oktoba lokacin da ake tantance fasinjoji da suka sauka a jirgin KLM daga ƙasar Kanada a filin Jirgin Saman Murtala Muhammad dake Lagos.
Babafemi ya ƙara da cewa an kama Munju da ƙunshi 74 na ƙwayar dake da nauyin kilogiram 35.20 a cikin biyu daga cikin jakunkuna uku da take ɗauke da su.
A jawabinta ta ce an ɗauke ta aikin kawo kayan ne zuwa Lagos inda aka yi mata alƙawarin bata Dalar Kanada 10,000.
Ta ƙara tana bukatar kuɗin domin biyan kuɗin karatun ta abun ya sa ta amince da tayin da aka yi mata kenan.