NDLEA ta kama wasu maniyyata da suka yi niyar safarar hodar ibilis zuwa ƙasar Saudiyya

Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi ta kama wasu maniyyata su huɗu ɗauke da wata hoda da ake kyautata zaton hodar ibilis ce.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Usman Kamorudeen, Olasunkanmi Owolabi, Fatai Yekini, da kuma Ayinla Kemi.

A wata sanarwa ranar Alhamis, Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya ce an kama mutanen ne a ɗakin wani otal lokacin da suke haɗiye ƙunshin ƙwayar hodar ibilis ɗin gabanin tashin su zuwa ƙasar Saudiya a ranar Laraba.

“Mutane huɗun da ake zargi an ajiye su ne a wani otal inda aka shirya musu ƙunshin ƙwayar hodar ibilis guda 200 mai nauyin kilogiram 220 domin su haɗiye a lokacin da jami’an NDLEA suka farma ɗakin,”

Sanarwar ta ƙara da cewa an gano ƙunshi 100 a kowane ɗaki inda mutane biyu za su haɗiye 100 kowannensu.

Tuni shugaban hukumar ta NDLEA, Buba Marwa ya yabawa jami’an hukumar na jihar Lagos kan kamen da suka yi.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...