NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa da ya haɗiye ƙunshi 111 na hodar ibilis  a filin jirgin saman Abuja

Jami’an Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Orjinze wani ɗan kasuwa akan hanyarsa ta zuwa ƙasar Faransa bayan da aka same shi da haɗiyar ƙunshin hodar ibilis 111.

A wata sanarwa ranar Lahadi, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya ce Orjinze ya yi iƙirarin cewa shi shi ɗan kwallon kafa ne da yake zaune a Turai.

An kama shi a ranar 21 ga watan Mayu a filin jirgi jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja lokacin da ake tantance fasinjojin da za su hau jirgin saman AirFrance mai namba 878 da zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris.

Babafemi ya ce bayan na’urar ɗaukar hoton jikin mutum ta tabbatar da cewa ya haɗiye haramtacciyar ƙwayar an tsare Orjinze inda ya kasayar da ƙunshi 111 na hodar ibilis a cikin tsawon kwanaki uku da nauyinta ya kai kilogiram 1.603.

More from this stream

Recomended