
Hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta sanar da kama wani mai suna, Muhammad Sani dan shekara 38 wanda ake zarginsa da yin safarar miyagun kwayoyi ga yan fashin daji a jihar Niger.
Hukumar ta NDLEA ta ce Sani wanda aka fi sani da suna Gamboli babban mai samarwa da yan bindiga miyagun kwayoyi ne a karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya ce jami’an hukumar sun gano nau’in ganyen ranar wiwi da ake kira da Skunk wanda ke da nauyin kilogiram 471.8 a gidan Sani dake Makera a Kuta ta jihar Niger a ranar 20 ga watan Nuwamba.
Femi ya ce Gamboli ya tsere lokacin da jami’an suka kai samame gidansa a lokacin.
A ranar 11 ga watan Disamba ne jami’an hukumar suka samu nasarar kama shi bayan da suka shafe kwanaki suna farautarsa.

