NCAA ta amince kamfanin Max Air ya cigaba da zirga-zirga

Biyo bayan kammala cikakken bincike kan halin da kamfanin jiragen sama na Max Air yake ciki hukumar NCAA dake lura da zirga-zirga jiragen sama a Najeriya ta sahalewa kamfanin cigaba da aiki kamar yadda yake yi a baya.

Idan za a iya tunawa kamfanin Max Air ya dakatar da zirga-zirga na tsawon watanni uku biyo bayan wasu jerin matsaloli da jiragen kamfanin suka samu ciki har da fashewar taya lokacin da jirgin ke ƙoƙarin sauka a Kano.

Hukumar ta NCAA ta yi maraba da matakin da kamfanin na Max Air ya É—auka biyo bayan faruwar lamarin.

Daraktan hulÉ—a da Æ´an jaridu na NCAA, Michael Achimugu ya faÉ—awa jaridar Leadership a ranar Litinin cewa a lokacin dakatarwar hukumar ta gudanar da cikakken bincike kan matakan kariya da kuma kan bakin É—ayan yadda kamfanin yake gudanar da aikinsa.

Binciken ya gano cewa kamfanin da kwararrun ma’aikata, wadatar kuÉ—i da kuma cikakken tsarin tafiyar da aiki hakan yasa zai iya cigaba da gudanar da aikinsa.

More from this stream

Recomended