Biyo bayan musayar yawu da yaki ci yaƙi cinyewa tsakanin yan Kannywood sakamakon hirar da aka yi da Tambaya a gidan rediyon BBC, Nazir Sarkin Waka ya yi alkawarin bata naira miliyan biyu.
Naziru ya bayyana haka ne cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.
Har ila yau ya yi kyautar naira miliyan daya ga jaruma Fati Slow Motion.
A ƙarshe ya bada hakuri ga mutanen da basu ji dadin kalaman da ya yi ba inda ya ce ya yi su ne badan ya batawa wasu rai ba.