Najeriya: Yunwa ta kashe yara 33 a Borno-MSF

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

MSF ta ce yaran na cikin matsanancin hali a sansanin ‘yan gudun hijira na Bama

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce ta kaddamar da taimakon gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya bayan mutuwar yara akalla 33 a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Borno.

MSF ta ce yaran sun mutu ne tsakanin ranakun 2 zuwa 15 ga watan Agusta a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke Bama a Jihar Borno.

An kiyasta cewa akwai yara kusan dubu shida ‘yan kasa da shekara 5 a sansanin da ke fuskantar wannan barazanar.

MSF ta ce a yanzu ta soma ba da tallafin gaggawa na abinci mai gina jiki, da magunguna tsakanin yaran da ke sansanin.

Ana dangata yanayin damina da karuwar matsalolin lafiya irinsu zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka masu yaduwa a sansanin.

Sai dai Hukumar bada agajin gaggawa NEMA ta ce tana sane da karuwar tamowa a sansanin na Bama, amma ta musanta mutuwar adadin wadanan yara kamar yadda MSF ke cewa.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...