Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Ya kuma ba da umarnin dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar ta Nijar nan take.
“Shugaba Tinubu ya kuma amince da dage takunkumin kudi da tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Guinea,” in ji wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta zo ne da taken ‘Najeriya ta bude iyakokin kasa da ta sama da jamhuriyar Nijar, tare da dage wasu takunkumin.