Najeriya: Labaran da suka shahara a ƙasar a makon da ya gabata | BBC Hausa

A kowane mako, mukan yi waiwaye kan abubuwan da suka faru a makon da ya gabata, inda muke zaɓo muku labaran da suka fi shahara.

A wannan makon, batun Ƙarin farashin wutar lantarki da man fetir da kuma batun caccakar da wasu suka yi ga gwamnatin Najeriya na daga cikin labaran da suka fi shahara.

Ƙarin farashin wutar lantarki da man fetir a Najeriya

Makon da ya gabata ya kasance mai ƙunci ga wasu ‘yan Najeriya, sakamakon ƙrin kudin da aka yi na farashin man fetir da kuma wutar lantarki a ƙasar.

A ranar Talata 1 ga watan Satumba ne ‘yan ƙasar suka wayi gari da labarin ƙarin farashin wutar, sai kuma a ranar Laraba kwatsam sai kuma aka samu labarin ƙarin farashin man fetir a ƙasar.

Ƙarin farashin dai ya jawo martani daban daban daga ‘yan ƙasar inda da dama daga cikinsu suka fara suka da caccakar shugaban a shafukan sada zumunta.

Har wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu sun yi barazanar zanga-zanga idan ba a mayar da farashin yadda yake a da ba.

Nuna mana aikin da ka yi wa arewacin Najeriya – ‘Yan Twitter ga Buhari

A makon da ya gabata ne matasa da dama ‘yan arewacin Najeriya suka harzuƙa a shafukan sada zumunta musamman Twitter, inda suke ta tambayoyi da amayar da abin da ke cikinsu kan gwamnatin Shugaba Buhari.

Da alama wasu ‘yan ƙasar ba su gamsu da kamun ludayin gwamnatin ƙasar ba ne shi yasa suke caccakar mulkin shugaban.

‘Yan ƙasar musamman waɗanda suka fito daga arewaci suna amfani da maudu’in #NorthernProjects, inda suka kafe kan cewa kusan dukkan ayyukan da shugaban ƙasar ya yi alƙawarin zai yi bai cika su ba.

Sakamakon harzuƙar da wasu ‘yan ƙasar suka yi, har suna cewa gwara gwamnatin jiya da ta yau a ƙasar.

An yi kashe-kashe tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan ISWAP a jihar Borno

A makon da ya gabata ne ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya ta ISWAP ta ce mayaƙanta sun kashe sojojin Najeriya aƙalla 20 a hare-hare biyu da suka kai kan sojojin a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Rahotanni na cewa masu tayar da ƙayar bayan cikin motoci da aka girke manyan bindigogi a kansu, sun kai hari ne a wani sansanin soji da ke Magumeri, kimanin kilomita hamsin daga Maiduguri babban birnin Jihar ta Borno.

To sai dai a wani ɓangaren, rundunar sojin ƙasar ta yi iƙirarin kashe mayaƙan ƙungiyar ta ISWAP a wani farmaki ta sama da dakarunta suka kai da jiragen yaƙi kan matsugunan masu tayar da ƙayar bayan a ƙauyen Kaza, kusa da Gulumba-Gana a yankin Bama cikin jihar ta Borno.

Shi ma farmakin, a ranar Talata sojojin suka kai, wato ranar da ƙungiyar ta ISWAP ta yi iƙirarin kashe sojojin.

Ambaliyar ruwa ta nutsar da mata da yara Kebbi

A makon da ya gabata ne wasu mata da ƙananan yara takwas suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke ƙaramar hukumar Jega ta Jihar Kebbi.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta bayyana cewa lamarin ya rutsa ne da matan da suka tashi daga ƙauyen Tungan Gaheru a ranar Litinin yayin da suke kan hanyar zuwa wajen wani biki a wani ƙauye da ke tsallaken kogi.

Matan sun nutse a ruwa ne yayin da suke ƙoƙarin hawa kwale-kwalen bayan an ajiye su a wani tsibiri sakamakon kaɗawar igiyar ruwa.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Kebbi Alhaji Sani Dododo ya shaida wa BBC cewa an ceto mata biyu, an kuma ga gawar mata uku, sannan ana neman gawar mace daya dayar uku.

An ɗaura auren ‘yar shugaban Najeriya

A ranar Juma’a ne aka ɗaura auren ‘yar gidan Shugaban Najeriya, Hanan Buhari, da kuma angonta Mohammed Turad, a fadar shugaban da ke Abuja.

Tun a watan Agustan da ya gabata ne rahotanni suka karaɗe shafukan sada zumuntar ƙasar cewa ƴar Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan, za ta auri ɗan fitaccen ɗan siyasar nan a Kaduna Sani Sha’aban wato Mohammed Turad.

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta wallafa hotunan auren, inda ta rubuta “#HamadForever Alhamdullilah”.

Muhammad Turad Sha’aban, wanda shi ne angon Hanan Buhari, ɗan tsohon ɗan majalisar da ya wakilci yankin Sabon Gari ta Zariya ne a majalisar dokoki ta biyar ta Najeriya, kuma ya yi takarar gwamna a zaɓukan 2007 da 2011.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...