
Hakkin mallakar hoto
@jidesanwoolu
Hukumomin Najeriya ba su yi karin haske kan yadda za a yi da mutumin ba, bayan sallamarsa daga asibiti
Gwamnatin jihar Legas ta ba da sanarwar cewa an sallami dan kasar Italiyan nan da aka tabbatar shi ne mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Gwamna Sanwo-Olu ya wallafa hotunan likitocin asibitin kula da cutuka masu yaduwa na Yaba tare da baturen Italiyan yana sanye da riga da gajeren wando da farar safa, a tsakiyar jami’an lafiyan.
Ba a bayyana fuska ko sunan dan kasar Italiyan ba, kuma duk da yake da duhun dare a lokacin amma ana iya ganinsa tsaye kyam da kafafuwansa ya rike hannuwansa.
A wani hoton kuma, an gan shi tare da sauran ma’aikatan lafiyan, kowannensu ya daga hannuwansa ga alama suna yin tafi.
Duk da an rufe fuskarsa, amma ga alama yanayi ne na farin ciki da murna a wani wuri mai kama da haraba ko farfajiyar wani gini.
Gwamna Sanwo Olu ya ce maras lafiyan ya yaba wa jami’an saboda kulawa ta musamman da goyon bayan da suka ba shi, kuma “cikin matukar farin ciki, jami’an cibiyar ayyukan gaggawar suka yi bankwana da mutumin” wanda ya shafe kimanin mako uku yana jinya.
Babajide Sanwo-olu ya ce ta hanyar kokarin hadin gwiwa tsakanin hukumomin lafiya na jihar Legas da Ogun da kuma na tarayya, sun iya takaita yaduwar kwayar cutar tsakanin mutumin da ya warke din, da wani wanda ya yi hulda da shi.
Mutumin dan kasar Italiyan ya zo Najeriya ne ranar 24 ga watan Fabrairu daga birnin Milan, kuma Hukumomi a ranar Alhamis 27 ga wata sun ba da sanarwar cewa an tabbatar ya kamu da cutar coronavirus karon farko a kasar.
Coronavirus, wata annoba ce gama duniya da zuwa yanzu ba a iya gano maganinta ba, kuma a ranar Juma’a wata cibiya a Amurka ta ce cutar ta yi sanadin kimanin mutum 10,000 a fadin duniya.
Sai dai, gwamnan Legas ya ambaci wani nau’in jini mai suna plasma, da ya ce mutumin da ya warke ya amince ya bai wa asibitin gudunmawar wani kaso daga jikinsa, kafin a sallame shi.
A cewarsa, jinin na plasma na kunshe da sinadaran gina jiki na proteins kuma wata garkuwar jiki ce da ke yakar kwayoyin cutar covid19 ko kuma coronavirus.
Sanwo-Olu ya ce jinin yana nan sun daskarar da shi a dakin ajiyar jini na jihar Legas kuma zai yi amfani wajen yi wa sabbin masu fama da cutar coronavirus da aka samu magani.
Gwamnan ya ce jami’an lafiyar Najeriya sun yi nasarar datse yaduwar kwayar cutar ta dalilin dan kasar Italiyan a kan mutum daya kacal, da ya yi hulda da shi.
Hakkin mallakar hoto
@jidesanwoolu
Kuma sun samu wannan nasara ce ta hanyar gagarumin aikin bibiyar abokan huldar mai warkewar da kuma dabarun katange cutar.
Sai dai ya ce a yanzu suna da sabbin wadanda suka kamu da cutar da dama kuma wadanda su ma shigo da ita suka yi Najeriya, don haka ya yi fatan ci gaba da amfani da irin dabarar da suka yi amfani da ita a kan mutumin da ya warke ta hanyar karfafa gwiwar mutane su rika yi nesa-nesa da juna don rage bazuwar cutar.
Mutumin dai ya isa Najeriya ne ta filin jirgin sama na Legas kafin washe gari ya wuce jihar Ogun mai makwabtaka.
Kwanansa biyu a Najeriya kafin a gano alamun coronavirus a tare da shi, sannan aka killace shi.